News
Kudirin dokar kafa ƴan sandan jihohi ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai
DAGA KHADIJA NASIR
Kudirin dokar kafa ‘yan sandan jihohi ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar a ranar Talata bayan doguwar muhawara.
Kudirin wanda mataimakin kakakin majalisar, Ben Kalu da wasu 14 suka dauki nauyinsa, na da nufin yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar na 1999, ta hanyar maida ikon ƴan sanda a ƙarkashin jihohi.
Kudirin ya kuma nemi kafa hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda na Jihohi daban-daban da hukumar ‘yan sanda ta tarayya.
Bugu da kari, na neman baiwa gwamnatin tarayya damar bayar da tallafi ga jihohi don tallafawa kafa rundunar ‘yan sanda ga kowace jiha.
Mukhtar Shagaya da daya ne daga cikin waɗanda suka ɗauki bauyin wannan ƙudiri ya ce ” Wannan kudiri zai kawo karshen matsalolin tsaro da ake fama da shi a kasar nan ta hanyar baiwa jihohi ikon kafa rundunar, da kuma tsara aikin su ta yadda aikinnsu zai inganta daidai da yanayin kowace jiha, maimakon yadda ake yanzu, sai an jira dole sako daga gwamnatin tarayya
Premium Times ta ruwaito cewa duka waɗanda suka yi magana kan wannan kudiri sun goyi bayan kirkiro da ƴan sandan jiha, suna masu cewa a baya wasunsu ba su amince da hakan ba saboda tsoron kada gwamnoni su rika amfani da su wajen muzguna wa abokan gaba.
Amma yanzu mun dawo rakiyar haka, muna goyon bayan kafa wannan runduna domin tsaro a jihohi da yawa a kasar nan ya taɓarbarewa.
