News
Hada Layuka Da NIN: Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Kulle Layukan Mutum Miliyan 4.2 A Nijeriya
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Kamfanin sadarwa ta MTN a Nijeriya ta ce ta katse layukan mutum miliyan 4.2 daga cikin turakarta, hakan na zuwa ne bayan da suka gaza hada lambar shaidar kasancewa dan kasa (NIN) da layukan wayoyinsu kafin zuwa karewar wa’adin ranar 28 ga watan Fabraru.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa hukumar kula da harkokin sadarwa a Nijeriya (NCC) ta bayar da umarnin cewa, dukkanin kamfanonin sadarwa da suke Nijeriya, su tabbatar da cewa dukkanin mutanen da suke amfani da layukansu na sadarwasu da suka kasa hada lambarsu da shaidar NIN to kai tsaye a kullesu kafin ranar 28 watan Fabrairun 2024. Bugu da kari, daidaikun mutanen da suka mika lambar shaidarsu na zama.
Kwastam ta kama harsasan da kudinsu ya kai Naira miliyan 557 da aka ɓoye a cikin buhunan Garin kwaki
‘Yan kasa NIN amma ba a samu lambar tantancewa ba, su kuma za a dakatar da layukan nasu ne ma gabaki daya. A gabar da aka hada layuka guda biyar ko fiye da lambar NIN da ba a tantance ba, lambar NIN din da aka gabatar ba tare da amincewa da su ba za a haramta amfani da su kafin ko zuwa ranar 29 ga watan Maris na 2024.
Kazalika, za a toshe layukan da suka hada lambarsu da NIN din da ba a tantance ba har sama da sau biyar zuwa ranar 15 ga watan Afrilun 2024.
Kafin a bude kowani layin da aka rufe, wajibi ne sai masu amfani da layukan su je a musu tantancewar zanen halitta kafin a saurari bude lambar tasu.
MTN a bayanin kudinta da ta fitar a ranar Juma’a ta ce, layukan da ta toshesu sun kasa gabatar da haidar kasancewarsu ‘yan kasa ne.
MTN a Nijeriya ta ce ta tantance layuka miliyan 19 tun lokacin da NCC ta bada umarni wa kamfanoni a watan Disamban 2023, da aka nemi su fara rufe layukan da ba su hada lambarsu da NIN ba. A cikin wannan adadin, layuka miliyan 4.3 an tantance kuma wasu miliyan 4.2 an katse su zuwa ranar 28 ga watan Fabraru a cewar MTN din.
Kamfanin ya kara da cewa, layukan da ya toshe su ba za su wani janyo wa kamfanin matsala kan kudaden shiganta ba domin kuwa ba wata daraja wajen samar wa kamfanin kudade suke ba.
Don haka ne, kamfanin ta bukaci dukkanin kwastominta da su gaggauta kasa cike dukkanin abubuwan bukata wajen hada lambobin tantancewar bankunansu da na shaidar NIN da asusun ajiyarsu.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
