Connect with us

News

Yan sanda sun kama shugaban makarantar bisa zargin yi wa wata daliba bulala da kuma raunata

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Rundunar ‘yan sanda ta cafke wani  shugabar makarantar sakandare a unguwar Igando da ke Legas bisa zargin yi wa wata daliba bulala da kuma raunata a jikinta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin,  ne ya  shaidawa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN a ranar Asabar cewa rundunar ‘yan sandan Igando ta dauke shugaban makarantar a ranar Juma’a domin yi masa tambayoyi.

Hada Layuka Da NIN: Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Kulle Layukan Mutum Miliyan 4.2 A Nijeriya

Hundeyin ya ce ma’aikatar ilimi ta jihar Legas ita ma ta sa baki a lamarin, da nufin a binciki shugaban makarantar, tare da gurfanar da shi gaban kuliya, idan aka same shi da laifi.

Daily News24 ta ruwaito cewa wani faifan bidiyo ya bayyana a yanar gizo wanda ke nuna wata daliba da alamomi a jikinta, wanda ake zargin an yi mata bulala.

Advertisement

Hakan ya sa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas, kwamishinan ilimi, da kwamishinan matasa da ci gaban al’umma su sa baki a kan lamarin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending