Connect with us

News

Kisan Sojoji: Basaraken Da Ake Nema Ya Mika Kansa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kasa da sa’a 24 bayan fitar da sanarwar da hedkwatar tsaron Najeriya ta yi, basaraken, Clement Ikolo ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Delta inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta a kudu maso kudancin Najeriya ta ce Sarkin Masarautar Ewu a jihar Delta, Clement Ikolo ya mika kansa ga rundunar a ranar Alhamis.

Shugaba Tinubu ya roƙi malaman addini su dinga yi wa Nijeriya addu’ar gyara maimakon tsine mata a wa’azinsu

Ikolo wanda basarake ne a karamar hukumar Ughelli a jihar ta Delta, na daya daga cikin mutum takwas da Hedkwatar Tsaron Najeriya ta fitar da sanarwar tana neman su ruwa a jallo.

Advertisement

Mutanen sun hada da Farfesa. Ekpekpo Arthur, Andaowei Dennis Bakriri, Akevwru Daniel Omotegbo (Aka Amagben), Akata Malawa David, Sinclear Oliki; Clement Ikolo Oghenerukeywe; Reuben Baru da Igoli Ebi.

“Hotunan mutanen da ake nema game da hannu a kisan sojojin Najeriya 17 a Ukuama da ke karamar hukumar Ugheli ta kudu a jihar Delta a ranar 14 ga watan Maris.” Sanarwar da hedkwatar tsaron Najeriyar ta wallafa a ranar Alhamis a shafinta na Facebook ta ce, hade da hotunansu.

Advertisement

Daga cikin mutanen akwai maza bakwai da mace daya.

Sai dai kasa da sa’a 24 basarake Ikolo ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar.

Advertisement

Gidan talbijin din Channels ya ruwato cewa da misalin karfe 6:41 na yamma basaraken ya kai kansa ga ‘yan sandan.

 

Advertisement

Jaridar Leadership ta ce Ikolo ya gana da manema labarai gabanin mika kansa inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.

A ranar 14 ga watan Maris wasu matasa suka halaka sojojin Najeriya 17 cikinsu har da manyan ofisoshi hudu a yankin Ukuama a jihar ta Delta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending