Connect with us

News

An rufe Jami’ar Jihar Plateau bayan mutuwar wani ɗalibi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Jami’ar Jihar Filato, da ke Bokkos, ta dakatar da dukkan harkokin koyarwa a makarantar har na tsawon kwanaki goma, bayan wani hari da aka kai da ya hallaka wani ɗalibi.

Advertisement

Ɗalibin wanda ke matakin aji biyu (200 level) a fannin kimiyyar na’ura mai kwakwalwa ya gamu da ajalinsa ne ranar Juma’a a harin da wasu suka kai harabra jami’ar.

Hukumar NDLEA Ta Cafke Mai Ciki Da Kudin Jabu Naira Miliyan 3.2

Wani malamin jami’ar, Yakubu Ayuba, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce, “Bayan wani abin bakin ciki da ya faru a jami’ar Jihar Filato, Bokkos, da kewaye a ranar Juma’a, 19 ga Afrilu, 2024; kuma bisa la’akari da illolin da wannan al’amari zai yi wa ɗalibai da ma’aikatan jami’ar, hukumar gudnarwa ta ɗauki matakin rufe jami’ar na tsawon kwanaki 10 daga ranar 19 ga Afrilu, 2024.

Advertisement

Yakubu ya ce an yi haka ne don ba da dama na ganin yanayin tsaro ya inganta a jama’ar.

“Don haka, an dakatar da jarabawar zangon karatu na farko da ake ci gaba da yi, inda za a koma rubuta ta ranar Alhamis 2 ga watan Mayu, 2024,” in ji shi.

Advertisement

Bugu da kari, jami’ar ta kuma samar da motocin bas don kai ɗaliban da za su maƙale zuwa Barikin Ladi.

Bbc ta Hausa ta ruwaito cewa a ranar Juma’a ne, wasu ‘yan bindiga suka kai hari a kauyukan Mangu da Bokkos inda aka ce an kashe mutane 15 a yankunan.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending