News
Farashin Litar Man Fetur Ya Haura Naira 1,400 A Kauyen Kano
DAGA MUHAMMAD BASHIR MUSA
Al’umma na ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin man fetur a faɗin Najeriya abin da ya sa masu sayar da man a kasuwar bayan fage ke cin karensu babu babbaka inda har suke sayar da shi kan N1,400 duk lita ɗaya a wasu yankunan ko kuma sama da haka.
Tun makon da ya gabata ake ganin dogayen layuka na ababen hawa a gidajen man da ke sayarwa, yayin da wasu kuma suke kulle saboda ba sa sayarwa.
A jihar Kano abubuwa sun fara sauyawa mazauna yankunan karkara, sakamakon yadda lamarin a wajen su yafi ƙamari.
Akan siyar da litar man fetur akan Naira N900 a cikin birni, amma a yankunan karkara ba haka abin yake ba.
Wani kauye mai suna Fulatan dake karamar hukumar rogo a jihar Kano da Jaridar Inda Ranka ta iske yadda ake siyar da farashin kowace lita kan Naira 1400 koma sama da haka a wasu wuraren.
Hakan ya sanya al’ummar yankin kira ga mahukunta domin taimaka musu, da nufin samar musu da mafita kan tsadar man.
Yawancin mazauna yankin babura ne da su masu kafa biyu, hakan ya sanya suke yawan shan man akai akai domin sufuri da Jigilar amfanin gona.
