Connect with us

News

Hukumar NDLEA Ta Kama Wani Fasinja Ɗauke Da Kwayar Tramadol 4,000 A Filin Jirgin Sama 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani fasinja dauke da kwayoyin tramadol 4,000 a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Ikeja, Legas.

Advertisement

Leadership ta ruwaito cewa Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Farashin Litar Man Fetur Ya Haura Naira 1,400 A Kauyen Kano 

Babafemi ya ce jami’an NDLEA da ke kofar ‘C ‘ ta filin tashi da saukar jiragen sama na Legas a ranar Juma’a sun dakile yunkurin wani da ake zargi na fita da kwayoyi zuwa Malpensa, Italiya a cikin jirgin Ethiopian Airline.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending