News
Ba’Amurken nan na farko da a tarihi aka taɓa yi wa dashen ƙodar alade, ya mutu watanni biyu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ba’Amurken nan na farko da a tarihi aka taɓa yi wa dashen ƙodar alade, ya mutu watanni biyu bayan an yi masa dashen.
Cikin watan Maris ne Babban Asibitin Massachusetts a Amurka ya yi wa Rick Slayman Mai shekaru 62 a duniya dashen ƙoda, bayan ya daɗe ya na fama da ciwon ƙoda.
Wani Matashi Ya Yi Wa ’Yar Uwarsa Mai Shekara 6 Yankan Rago Da Reza A Zariya
Hakan ne ya sa asibitin ya yi masa dashen ƙodar alade, kuma ya rayu har tsawon kusan watanni biyu.
Labarin dashen dashen ƙodar ya karaɗe duniya a lokacin da aka yi wa Riok, domin shi ne na farko da aka sa wa ƙodar wani dabba a kasancewar sa mutum.
Sai dai kuma rahoronni sun nuna cewa mutuwar Slayman ba ta da nasaba da matsalar dashen ƙodar da aka yi masa. Haka dai asibitin ya ruwaito.
“Iyalan mu sun cika da jimami da alhinin mutuwar Rick, amma farin cikin mu shi ne da ya kasance mutumin da ya ƙarfafa wa mutane da dama gwiwar cewa za su iya yin nasara kan abin da suke da yaƙini kan sa.” Haka iyalan suka bayyana a ranar Lahadi.
Premium Times ta ruwaito cewa Iyalan na Slayman sun jaddada godiya ga likitocin da suka yi wa Slayman dashen ƙoda da waɗanda suka riƙa kula da shi.
Dama dai shi ma aladen sai da aka yi masa dabarun likitoci na zamani, ta hanyar cire masa duk wasu ƙwayoyin halittu masu illa
