Connect with us

News

An Kama Wasu Mutane Uku Da Ke Kokarin Shigar Da Kwayoyi Ofishin ‘Yan Sanda a Cikin burodi

Published

on

SAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da yunkurin safarar miyagun kwayoyi da aka boye a cikin biredi zuwa wani da ake zargi da hannu a hannun ‘yan sanda.

Advertisement

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mansir Hassan, ASP, ya ce an samu mutanen uku da wani adadin kwayoyi da ba a tantance adadinsu ba a boye a cikin biredi.

A yau mahajatta daga Fagge, Gwale, Dala da Ungogo za su tafi kasa mai tsarki 

Hassan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kaduna ranar Lahadi, ya bayyana sunayen wadanda ake zargin John Solomon (namiji mai shekaru 38), Kunle Oluwale (namiji mai shekaru 45) da James Daniel Baba (namiji mai shekaru 45).

Advertisement

A cewarsa, mutane ukun da ake zargin dukkansu mazauna Sabon Wuse ta Abuja ne, an kama su ne a dakin Bincike na sashin binciken manyan laifuka na jihar Kaduna.

A halin da ake ciki, bayan kama mutanen uku, kakakin rundunar ‘yan sandan ya rawaito kwamishinan ‘yan sandan jihar, Audu Dabigi, ya gargadi jami’an da ke bakin aiki da su kasance cikin shiri da lura domin kaucewa afkuwar lamarin.

Advertisement

Hassan a cikin sanarwar ya ce, “Hukumar binciken manyan laifuka ta jihar Kaduna (SCID) ta kama wasu mutane uku da ake zargi da yunkurin kai wa wani da ake zargi da laifin safarar miyagun kwayoyi a hannun ‘yan sanda.

“Wadanda ake zargin sun hada da John Solomon (namiji mai shekaru 38) Kunle Oluwale (namiji mai shekaru 45) da James Daniel Baba (namiji mai shekaru 45), dukkansu mazauna Sabon Wuse, Abuja, an kama su ne a dakin Bincike na SCID Kaduna.

Advertisement

“An samu wadanda ake zargin dauke da wayar salular Bomtel da wasu kwayoyin da ba a tantance adadinsu ba a boye a cikin biredi. Sun yi yunkurin shawo kan jami’in Bincike na (CRO) da ya kai wa wani Gideon Amao biredin, wanda ake zargin da hukumar SCID ke bincike a halin yanzu.

“An dauki hotunan wadanda ake zargin da kuma abubuwan da aka kwato. Ana ci gaba da binciken, kuma za a sanar da ci gaban a kan lokaci.

Advertisement

“Kwamishanan ‘yan sanda, Audu Dabigi, ya gargadi jami’an da su kasance cikin shiri da lura domin gujewa duk wani abu marar dadi daga faruwa.”

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending