Connect with us

News

Ansa Tsauraran Matakan  Tsaro Bayan Fara Shari’a Kan Rikicin Masarautar Kano

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

An tsauraran matakan tsaro a harabar babbar kotun tarayya da ke zamanta a kan titin Court Road da ke Jihar Kano, yayin da aka fara sauraren karar rikicin masarautar jihar.

Advertisement

LEADERSHIP ta ruwaito cewa, ‘yansanda da jami’an hukumar DSS, sun girke motocinsu a kan hanya tare da hana zirga-zirga.

Sarkin Kano Alhaji Dr Ado Bayero Ya Cika Shekara 10 Da Rasuwa

Masu ababen hawa na bin hanyar Gyadi-Gyadi ko Zoo Road domin kaucewa cunkoso.

Advertisement

Yajin aikin da aka yi na kwanaki biyu ne, ya hana zaman babbar kotun, kan batun dawo da Sarki Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta bayar da umarnin dakatar da gwamnatin Jihar Kano daga aiwatar da dokar da ta rushe masarautun jihar.

Advertisement

Mai shari’a Mohammed Liman ya bayar da wannan umarni ne, bayan da Sarkin Dawaki Babba, Alhaji Aminu Babba Dan Agundi ya shigar da kara.

An shirya fara zaman kotun da misalin karfe 10 na safe, a ranar Alhamis, amma aka sauya lokaci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending