News
Talakawa Na Fama da Tsadar Rayuwa :‘Yan Majalisa Sun Bukaci Gwamatin Tarraya Ta Gaggauta siyawa Shugaba Tinubu da Shettima sabbin Jirage
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN TUKUNTAWA
Kwamitin tsaro a majalisar dokokin Najeriya ya bukaci gwamnatin tarayya ta gaggauta siyan sabon jirgin sama domin amfanin shugaban kasa, Bola Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima.
Premium Times ta ruwaito cewa Hakan na kunse ne a cikin wani rahoto da kwamitin ya fitar bayan sauraron halin da jiragen saman shugaban kasa ke ciki ta fuskar amfani da su domin sufurin shugaban kasa da mataimakinsa.
Shirin TMP Zai Tura Na’urori 67 Zuwa Tashar Jiragen Ruwa Da Iyakokin Najeriya
“Wannan kwamitin yana da da ra’ayin cewa ya kamata a siyawa shugaban kasa da mataimakinsa sabon jirgi bayan gamsuwa cewa jiragen da suke amfani da su basu da koshin lafiya, a saboda haka ya kamata a gaggauta siyan karin sabbin jirage guda biyu domin tabbatar da tsaron shugabannin kasa,” a cewar rahoton kwamiti
Rahoton, mai dauke da sa hannun shugaban kwamitin, Ahmed Satomi, ya kara da cewa siyen sabbin jiragen zai fi sauki a kan kudin da ake kashewa wajen kula da tsofin jirage guda shida da ke jibge, kowanne da matsalarsa.
‘Yan bnajeriya sun sha yin korafi a kan yawan jiragen shugaban kasa wadanda ke lashe kudade masu yawa wajen kulawa da su.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya taba alkawarin cewa zai rage yawan jiragen ta hanyar siyar da wasu daga cikinsu amma hakan ba ta faru ba har ya sauka daga kan mulki.
Tuni kwamitin ya mika rahotonsa zuwa fadar shugaban kasa domin daukan mataki na gaba.
A ranar 23 ga watan Maris ne Honarabul Satomi ya fara gabatar da kudirin neman a sake siyan sabbin jiragen sama ga Tinubu da Shettima.
