News
Barazanar tsaro :Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Zai gabatar da sallar idi a masallacin kofar Mata .
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A wani al’amari na ban mamaki, tsohon Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya bayyana shirin gudanar da Sallar Idi a filin Idi na Kofar Mata da ke Kano, duk kuw da cewa an maye gurbinsa da Sarki Muhammadu Sanusi (II).
Sanarwar Hakan ta fito ne daga bakin babban kansilan Masarautar Abbas Sanusi,
A cewar sanarwar Hakan ya boyo soke gayyatar da aka yi masa tun farko zuwa bukukuwan Sallah, saboda dalilai na tsaro da kuma umarnin ‘ da hukumar yan sanda.ta bayar
Jaridar historical ta rawaito cewa Majalisar Masarautar Kano mai dauke da kwanan watan Yuni 14, 2024, inda ta bukaci Hakimai da shugabannin gargajiya da su halarci Sallar Idi da misalin karfe 8:00 na safe ranar Lahadi.
Ana dai kallon matakin a matsayin kalubale ga ikon mai martaba sarki Muhammadu Sanusi (II) wanda shi ma ake sa ran zai jagoranci sallar idi a wurin.
Lamarin dai ya sanya ayar tambaya kan sahihancin sarakunan biyu da kuma yiwuwar rikici a jihar Kano.
Idan ba,amantaba jaridar inda ranka ta rawaito Rundunar ‘yan sanda ta soke bukukuwan babbar sallah , saboda dalilai na tsaro
Abin Jira a gani sai gobe babbar sallah aga Yadda Zata kasance
