News
Hukumar NDLEA Ta Kama Dillalan Ƙwayoyi Fiye Da Mutum 1,344 A Katsina
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa NDLEA reshen jihar Katsina ta bayyana kama mutane 1,344 da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da masu safarar sauran haramtattun kayayyaki a shekarar da ta gabata.
Kwamandan hukumar na jihar Katsina, Hassan Abubakar, shi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ranar Alhamis.
Daruruwan Mutane Sun Banka Wa Wani Mutum Wuta Bisa Batanci Ga Al-Qur’ani
Ya kuma ƙara da cewa hukumar ta kama jimillar kilogiram 1,319.258 na kayan maye daban-daban, da suka hada da Cannabis Sativa, kayan maye, da kuma sauran magungunan da aka hana Safarar su.
Channels TV ta ruwaito cewa Tattaunawar ya gudana ne a yayin da ake gudanar da shirin tunawa da ranar yaki da shan muggan ƙwayoyi da safarar su na majalisar ɗinkin Duniya.
Kwamandan ya ƙara da cewa, rundunar ta yi shirye shirye akan wayar da kan mutane sama da 56,000, tare da baiwa mutane 136 shawara, ta kuma yankewa 107 hukunci, tare da gabatar da sabbin kararraki 120 .
