Connect with us

News

Shugaban kungiyar Matan jami’an Kwastom ta COWA ta bukaci Dalibai su kaucewa dabi’ar shan miyagun kwayoyi

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Shugaban kungiyar matan jami’an hukumar hana fasa kwauri ta kasa (COWA) kuma matar babban konturola janar na hukumar kwastom, Misis Kikelomo Adewale Adeniyi a jiya Talata 25 ga watan Yuni ta bukaci yara da su rike muradansu na gyaran gobensu ta hanyar kaucewa ta’ammali da muggan kwayoyi.

Advertisement

Uwargidan kwanturola janar na Kwastom din tayi kiran ne yayin da ta jagoranci shugabanni da mambobin kungiyar COWA a gangamin wayar da kai kan illar shan miyagun kwayoyi a kananun makarantun sakandire guda 2 a Abuja wadanda suka hada da: Karamar Sakandire ta Garki da ta Karu a wani bangare na bikin ranar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta duniya.

Da DUMI DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Amfani Da Mazubin ‘Take Away’

Wata kungiya mai suna National Bridge and Bond Initiatives karkashin shugabancin Barista Festus Onifade ne suka shirya taron da hadin gwiwa da COWA inda aka fara a makarantar Sakandire ta Garki a inda ta yabawa makarantar da malamanta kan baiwa COWA damar wayar da kan dalibai.

Advertisement

“A wannan rana mai tarihu, kungiyar COWA ta ga ya zama dole tazo gare ku tare da karfafa gwiwarku wajen zama ‘yan kasa na gari. A yanzu haka ina ganin gwamnoni da shugaban kasa da ma matan jami’ai anan – don haka kar ku lalata rayuwarku ta hanyar fadawa shaye-shaye”, inji shugaban kungiyar.

Shugabar, wacce ta bayyana yaki da shan muggan kwayoyi a matsayin hakkin da ya rataya kan kowa da kowa ta karfafi gwiwar mata da su shiga a dama dasu a yaki da dabi’ar shan muggan kwayoyi domin samar da al’umma ta kwarai.

Advertisement

A gefe guda kuma shugabar ta COWA ta ziyarci karamar Sakandire ta Karu a Abuja inda tayi kira ga dalibai da su kaucewa shiga fagen shaye-shaye domin hakan na illa da lafiyarsu.

Ta ce ” A don haka muna shawartarku ku zama ‘yan kasa na gari. Ku dinga sauraron mahaifanku da malamanku, ku yi abinda zai gyara kasarku. Nayi farin ciki da yadda na ganku.”

Advertisement

 

Shugabar wacce ta bukaci daliban da su mayar da hankali kan karatunsu da zai taimaka su koyi ilimi da sana’a don gina gobensu ta ce “muna son ku taimaki kasarku ta hanyar kaucewa shan miyagun kwayoyi. Ku zama masu biyayya da kaucewa munanan dabi’u a makatanta ko a gida domin gyara al’ummarmu”.

Advertisement

 

Tun da farko, Barista Festus Onifade ya yabawa shugabar kungiyar ta COWA da tawagarta kan shirya taron.

Advertisement

Ana bikin ranar yaki da sha da ta’ammali da muggan kwayoyi ta duniya a duk ranar 26 ga watan Yuni domin wayar da kai kan illar shan miyagun kwayoyi.

Sannan ana yinta don daukar matakan fitar da al’umma daga shan miyagun kwayoyi.

Advertisement

Taken bikin na bana shi ne ” Hujja a bayyane: a dau matakan kariya’.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending