News
Da DUMI DUMI: Gwamnatin Tarayya Ta Haramta Amfani Da Mazubin ‘Take Away’
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarayya ta haramta amfani da robobin ‘Take Away’ a duk ma’aikatun gwamnati (MDAs).
DAILY TRUST ta ruwaito cewa Mazubin wanda ya kasance ana amfani da shi ne na lokaci ɗaya daga nan amfanin sa ya ƙare.
Mayakan Boko Haram Sun Yi Garkuwa Da Wani Alkakin Babbar Kotu Tare Da Matarsa Da Direbansa
Da yake jawabi ga manema labarai a majalisar zartarwa ta tarayya (FEC), a yau Talata, karamin ministan muhalli, Iziaq Adekunle Salako, ya ce dokar hana amfani da mazubin an ƙaƙaba ta ne don tafiyar da tsarin dq gwamnatin tarayya ta yi na ƙoƙarin sarrafa yawaitar bola.
Ya ce, “Wannan yunƙurin yana nuna ƙudurinmu na magance barazanar sauyin yanayi,mutuwar ƙananan halittu da kuma magance ƙazanta”.
Ministan ya bayyana tsananin gurbacewar da amfani da mazubin Take Away ya jawo a Najeriya, inda ya bayyana hakan a matsayin “babban al’amari da ya dame mu a kasarmu”.
Ya kuma ce haramcin yin amfani da mazubin a ma’aikatu shiri ne na tunkarar yawaitar amfani da robobi a fadin ƙasar nan.
-
Opinion6 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion6 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News4 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
