Connect with us

News

Ma’aikatan Lafiya Sun Tsinduma Yajin Aikin Gargadi A Kaduna

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ma’aikatan lafiya a jihar Kaduna sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.

Advertisement

Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ta yi a wasu asibitocin gwamnati ya nuna cewa likitoci da ma’aikatan dakin gwaje-gwaje ne kawai ke bakin aiki.

Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Ɓude Iyakokin Nijeriya  Domin Shigo Da Wasu Kayayyakin Abinci.

Sakamakon haka ne ya sa, aka sallami da yawa daga cikin majinyatan da ke asibitocin saboda babu masu kula da su.

Advertisement

Da yake jawwbi a wata hira da aka yi da shi ranar Litinin a Kaduna, Shugaban ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa a jihar, Mista Ishaku Yakubu, ya ce sun shiga Yajin aikin ne domin biyan wasu bukatun da suke nema a biya musu.

Ya ƙara da cewa akwai bukatu da aka mikawa gwamnatin jihar tsawon shekaru amma har yanzu basu ce komai ba.

Advertisement

Yakubu ya ce, “Ma’aikatan lafiya sun fara yajin aikin ne a kan batutuwan da har yanzu gwamnati ta ƙasa tsaida matsaya.

Ya ƙara da cewa har yanzu gwamnatin jihar ba ta fara biyan mualawus alawus ɗin da gwamnatin tarayya ta kaddamar ba tun shekarar 2003 .

Advertisement

Da aka tuntubi babbar sakatariyar ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Aishatu Mohamed-Saqid, ta ce za ce wani abu a hukumance dangane da wannan lamari.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Solacebase 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending