Connect with us

News

Dangote: akwai wasu mutane da basason matatar maina ta Fara aiki

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Attajirin nahiyar Africa Baki Daya alhaji Aliko dangote ya zargin wasu daga cikin kusushin gwamnatin Nigeria da basason  matatar mansa ta Fara aiki sabida San zuciyarsu kawai dan suna samun wani abu daga cikin man da Ake shigowa dashi Nigeria

Advertisement

 

Naso ace matatar maina ta Fara aiki dan talakan Nigeria ya samu saukin rayuwa Amman Hakan kamar  Abu ne Mai wuya domin  kuwa akwai wadan da basason  Haka

Advertisement

 

Attajirin mai kudi a Afirka, Aliko, ya ce daya daga cikin abokansa da ya fara zuba jari a kasashen waje shekaru hudu da suka wuce, yana yi masa gori a baya a ‘yan kwanakin nan.

Advertisement

Tun da farko Dangote ya ba da labarin yadda wani ke kokarin toshe hanyoyinsa na shigo da danyen mai da kuma yadda ake samun wahalar kayayyakin cikin sauki

Sai dai a makon da ya gabata, hukumar kula da man fetur ta Nijeriya (NMDPRA) ta ce har yanzu gwamnatin Nijeriya ba ta ba wa matatar man Dangote lasisin fara aiki a kasar ba

Advertisement

 

Farouk Ahmed, babban jami’in gudanarwa na hukumar NMDPRA, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis

Advertisement

A cewar Ahmed, ikirari da ake yi na durkusar da ayyukan matatar ta Dangote sakamakon rashin samar da danyen mai da kamfanonin mai na kasa da kasa ke yi ba gaskiya ba ne, ya kara da cewa matatar ta na nan a matakin farko kuma har yanzu ba a ba ta lasisi ba.

Ahmed ya kara da cewa man dizal din Dangote bai kai matsayin kasa da kasa ba, lamarin da dan kasuwar ya musanta a wata tattaunawa da yayi a karshen mako

Advertisement

A wata tattaunawa da ya yi da jaridar PREMIUM TIMES, Dangote ya bayyana yadda wani abokinsa da ya yi kokarin yin magana ya nuna kishin kasa a Nijeriya a yanzu yana yi masa ba’a.

 

Advertisement

Yace shekaru hudu da suka wuce, wani abokina ya fara saka kudinsa a kasashen waje. Ban yarda da shi ba, na kuma roke shi da ya sake tunanin matakin da ya dauka domin maslahar kasarsa.

 

Advertisement

Yace a kwanakin baya abokina ya gargade ni,da saka jari a Nijeriya yanzu kuma yanayin dariya.

Idan za,aiya tunawa jaridar inda ranka ta rawaito koda a kwanakin bayannnan saida Saida wasu daga cikin mambobin majalisar wakilai takai ziyara matatar ta dangote inda tace babu ingantattun kayan aiki Wanda Shi Kuma dangote da musunta Hakan

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending