News
Wasu ‘Ya’ya Da Suka Fusata Sun Raunata Mahaifinsu Tare Da Kashe Dan Uwansu A Jigawa.
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wasu ‘ya’ya maza biyu da suka fusata sun kashe dan uwansu tare da raunata mahaifinsu a karamar hukumar Kiyawa da ke jihar Jigawa.
Mazauna garin sun shaidawa Jaridar DAILY POST cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan uwan biyu da ke zargin dan uwansu da maita, suka yi masa duka da sanduna tare da raunata mahaifinsu a lokacin da ya yi yunkurin kubutar da shi.
Masu Sayar Da Mai Na Rufe Gidajen Mai A Yayin Da A Ke Shirin Zanga-zanga
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa: “A ranar 25 ga Yuli, 2024, da misalin karfe 12:30 na rana, bayanan sirri da rundunar mu ta samu sun bayyana cewa wasu mutane biyu Haruna Idi daga kauyen Garkon Alli da ke karamar hukumar Kiyawa da mahaifinsa mai shekaru 80, Idi Hassan, daga wannan adireshin, an yi masa mugun duka da sanduna. Sakamakon haka, wanda aka azabtar ya sami mummunan rauni.
“Bayan samun rahoton, jami’an tsaro na sashen Kiyawa sun garzaya zuwa wurin da lamarin ya faru inda suka kai wadanda abin ya shafa zuwa asibitin koyarwa na Rashid Shekoni Dutse domin kula da lafiyarsu.
“Daya daga cikin wadanda lamarin ya shafa, Haruna Idi ya rasu, kuma mahaifin wanda ya samu karaya a hannu da kafa, an kwantar da shi kuma yana asibiti yana karbar magani.”
DSP Shiisu Adam ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa wadanda ake zargin, Ahmadu Idi mai shekaru 45 da kuma Sale Idi mai shekaru 25 da ke kauyen Garkon Alli, sun hada baki da dan uwansu, inda suka zarge shi da maita.
Ya ce wadanda ake zargin sun kuma raunata mahaifinsu mai suna Idi Hassan, bayan da ya yi yunkurin ceto dansa.
Ya ce bayan kammala bincike a sashin binciken manyan laifuka na jiha dake Dutse, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.
