Connect with us

News

Gwamnan Kano Ya Sanar Da Naɗa Sabbin Hukumomin Zartarwa A Manyan Makarantun Jihar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A 31 ga Yuli, 2024, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da naɗa sabbin hukumomin zartarwa a manyan makarantun jihar. Waɗanda suka haɗa da Jami’ar Aliko Dangote, Wudil (KUST), Yusuf Maitama Sule University, Kano (NWU), da kuma makarantar fasaha ta Kano (Kano Polytechnic).

Advertisement

A Jami’ar Aliko Dangote, Wudil (KUST), an naɗa Justice Audu Aboki a matsayin Pro-Chancellor da Shugaban Majalisar Gudanarwa, tare da Prof. Ibrahim Bello Kano, Prof. Dije Muhammad Sulaiman, Dr. Fa’iza Mukhtar Adhama, Dr. Aminu Bello Wudil, Dr. Garba Abubakar, Alh. Sabi’u Bako, da wasu wakilai daga NUC da MHE, da kuma wasu wakilai 9 daga jami’ar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nemi Ganawa Da Masu Zanga-zanga

 

Advertisement

A Yusuf Maitama Sule University, Kano (NWU), an naɗa Prof. Hafizu Abubakar a matsayin Pro-Chancellor da Shugaban Majalisar Gudanarwa, tare da Hon. Nura Muhammad Dankadai, Haj. Mariya Kote, Dr. Kabiru Muhammad Kofa, Prof. Mustapha Hussaini, da wasu wakilai daga NUC, MHE, da jami’ar.

Hukumar Zartarwa ta Kano Polytechnic

Advertisement

A Kano Polytechnic, an naɗa Engr. Buba Galadima a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa, tare da Engr. Rasheeda Musa, Dr. Usman Abbas, Solicitor General na Ministan Shari’a, wakilai daga MHE da NBTE, Prof. Dahiru Sani Shu’aibu daga jami’ar, da wakilai daga kowacce makaranta a ƙarƙashin Kano Polytechnic.

An kuma tabbatar da Alh. Aliko Dangote a matsayin Chancellor na Aliko Dangote University, Wudil. Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata, Komishinan Ilimi Mai Zurfi, ya yi fatan alheri ga dukkan sabbin shugabannin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending