Connect with us

News

ZANGA-ZANGA: ‘Za Mu Murƙushe Duk Wani Kangararren Da Ya Nemi Tada Zaune Tsaye’ – Sufeto Janar Egbetokun

Published

on

Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta soki shugabannin kungiyar Take It Back Movement’, saboda sun ƙi cika sharuɗɗan bayar da bayanan su kamar yadda hukumar ‘yan sanda ta nemi shugabannin shirya zanga-zanga su yi a faɗin ƙasar nan.

Kayode Egbetokun ya ce ya bayar da umarni ga ‘yan sanda a faɗin ƙasar nan su fita su kare rayuka da dukiyoyin jama’a daga ɓatagarin da ka iya kai masu farmaki.

Kamfanin  WhatsApp na duba yiwuwar barin Najeriya

“Abin takaici masu shirya zanga-zanga ba su amince su bayar da bayanan sunayen su da adireshin su kamar yadda Dokar ‘Yan Sanda ta tanadar ba.” Inji Egbetokun.

“Shi kan sa sunan ƙungiyar, wai “Take It Back Movement bai dace da dimokraɗiyya ba, ba ya cikin tsarin kundin tsarin mulki, kuma haramtacce ne.”

Egbetokun ya umarci ‘yan sanda su murƙushe duk wani ki wasu kangararru da aka iya banka wa dukiyoyi wuta, yi wa jama’a barazana to mai kawo wa rayuwar jama’a da dukiyoyin su ko keta haddin da aka ƙayyade wa masu zanga-zanga.

Advertisement

A ƙarshen makon jiya ne Rundunar ‘Yan Sanda ta ce dokar ƙasa ta ba su ‘yancin sanin sunaye, asali da adireshin masu shirya zanga-zanga.

Premium Times ta ruwaito cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta kare kan ta dangane da sharuɗɗan da ta gindiya wa masu shirin zanga-zanga cewa su kai sunayen su da adireshin su da wasu bayanai wurin Kwanishinan ‘Yan Sandan jihohin su.

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, biyo bayan zargin da madugun kare haƙƙin jama’a, Deli Adeyanju da wasu ƙungiyoyin kare haƙƙi suka yi wa ‘yan sanda cewa wannan buƙatar da suka nema ta saɓa wa kundin dokokin Najeriya.

Ya ce ‘yan Najeriya na da haƙƙin fita yin zanga-zanga ta lumana, su kuma ‘yan sanda na da haƙƙi da nauyin da ya wajaba kan su na su kare rayuka, dukiyoyi da lafiyar jama’a.

A ƙarshen makon jiya ne dai Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya ce ”masu zanga-zanga su kai sunayen su da adireshin su Ofishin Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihohin su.”

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa za ta bari a fita zanga-zangar lumana, amma bisa waɗansu tsauraran sharuɗɗa da ta gindaya.

Advertisement

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ne ya sanar wa manema labarai sharuɗɗan da suka gindiya kafin masu fita zanga-zanga su fita a ranar 1 ga Agusta, kamar yadda suke ta shelar za su fita ɗin yawon kwanaki 10, wato har zuwa ranar 10 ga Agusta.

Da yake wa manema labarai ƙarin bayani a Hedikwatar ‘Yan Sanda da ke Abuja a ranar Juma’a, Egbetokun ya ce lallai masu fita zanga-zanga su na da ‘yancin fita, kamar yadda dokar ƙasa ta tanadar, amma fa ya kasance zanga-zanga ce ta lumana, sannan kuma zai kasance tilas a cika waɗannan sharuɗɗa da rundunar sa ta gindiya.

 

SHARUƊƊAN FITA ZANGA-ZANGA:

 

Sufeto Janar ya ce na farko masu fita zanga-zanga su rubuta wa Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar su wasiƙa mai ɗauke da cikakken bayanin abin da duk suka tsara za su yi yayin zanga-zanga.

Advertisement

Kuma ya kasance a cikin wasiƙar akwai jerin sunayen masu shirya ita zanga-zangar, wato jagororin ta a kowace jiha.

Ya ce an gindaya waɗannan sharuɗɗa ne domin jami’an tsaro su samu damar sa-ido sosai a lokacin ita wannan zanga-zanga ta lumana.

Ya ce jami’an tsaro na so su tabbatar cewa sun ƙare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Kafin su fara zanga-zanga su bayar da cikakken bayanan inda za su fara taruwar haɗa gangami da kuma titinan da za su bi.

“Kuma ana buƙatar sanin daidai lokacin da za su wanye zanga-zangar da kuma sunaye da adirwshin masu shirya zanga-zangar.”

Ya ce idan suka yi haka, to za a samu sauƙin tura jami’an tsaro a wuraren, domin su tabbatar cewa ɓatagari ba su yi amfani da zanga-zanga ɗin sun tayar da hargitsi ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending