News
An Tura Tsohon Shugaban Kasa Gidan Yari Na Tsawon Shekaru 20
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata kotu a ƙasar Guinea ta yanke wa tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Moussa Dadis Camara zaman gidan yari na tsawon shekaru 20 kan ta’addanci ga al’umma a ƙasar.
An yi masa hukuncin ne sakamakon jagorantar ɗaya daga cikin kashe-kashe mafi muni a tarihin ƙasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 156 a lokacin da jami’an soji su ka buɗe wa jama’a wuta a wani gangamin neman kawo ƙarshen mulkin soji a shekarar 2009.
Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa Ta Kano Pillars Ta Naɗa Sabon Koci
Camara ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar ne bayan wani juyin mulki a shekarar 2008 a lokacin da shugaba Lansana Conte ya mutu, wanda shi ne mafi daɗewa a karagar mulkin ƙasar.
Bayan kisan kiyashin ba da jimawa ba, Camara ya fice daga ƙasar sakamakon tsallake rijiya da baya da ya yi na harin kashe shi da aka yi.
Ya dawo ƙasar ne daga ƙasar Burkina Faso a Satumban 2022 inda ya yi iƙirarin ya na da hannu a cikin kisan kiyashin da aka yi a lokacin mulkin nasa.
An yanke wa Camara hukunci ne tare da wasu kwamandojinsa guda bakwai yayin da aka wanke wasu guda huɗu.
Haka nan, an kama camara ne laifukan kisan kai, fyaɗe, duka da kuma garkuwa waɗanda aka yi wa suna da ta’addanci ga Ɗan Adam.
