News
Zanga Zanga: Ban nemi taimakon kowa ba kamar yadda wasu mutanan ke yadawa —Alaramma Malam Sa’idu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Babban Majabakin Alkur,ani Mai girma a Masallaci Alfur,kan dake Kano Alaramma Malam Sa’idu Hassan Haruna wanda matasa kewa lakabi da mai “Golden Voice” ya nuna takaicinsa kan yadda ake ta yada Asusun Bankinsa a kafafan sada zumunta akan yana neman taimako ba tare da izininsa ba.
Malam Sa,idu ya bayyana hakan ne a yayin tataunawa Gidan Rediyon Freedom da ke jihar Kano
Malam ya ce yana mamakin yadda wasu daga cikin Jama,a suke ta yada labarin karya akan yana neman taimako agun al,umma ta hanyar amfani da account number sa a shafin kan sada zumunta.
Ya kara da cewa tabbas account din da aketa yadawa na shine amma bashida masaniyar ko su wane sukai wannan aikin amman yace baya neman taimakon kowa.
Malam Sa,idu ya ce shi taimakon Allah yake nema adan haka baya neman taimakon kowa kuma yayi adduar, Allah ya kawo saukin Wannan lamarin zanga zanga da akafara jiya fadin Najeriya.
Malam Sa,idu dai yana daga cikin wadanda bata gari daga cikin masuyin zanga zanga suka shiga shagon Sana,arsa inda suka sace kayayyakin Sana,arsa .
