Connect with us

News

KANO:  ‘Yan Sanda Sun Fara Bi Gida-Gida Suna Farautar Kayan Da Aka Wawushe Yayin Zanga-Zanga 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Jami’an Rundunar ƴan Sandan Jihar Kano sun kaddamar da bincike gida-gida a wani yunkuri na kwato wasu kayayyakin da aka sace a lokacin zanga-zangar adawa da salon Mulkin Shugaba Tinubu a Kano

Advertisement

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito yadda wasu da ake zargin ƴan daba ne suka yi uwa makarɓiya da lamarin zanga-zangar da ta fara cikin kwanciyar hankali da lumana.

Cacar Baki Ta Balle Tsakanin Jamiyyar APC Da Kuma Jamiyyar NNPP A Kano Kan Masu Zanga Zanga

Sun kai samame a ma’ajiyar abinci, da shaguna, da Ofisoshinmu Gwamnati kamar yadda aka yi wa Ofishin hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) da ba a ma ƙaddamar da ita ba inda aka kwashe duka kayan da ke ciki.

Advertisement

Ƴan zanga-zangar sun kuma lalata fitulun kan titi da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen kawata wuraren taruwar jama’a.

Sai dai Rundunar ƴan Sandan ta dauki matakin damke mutane sama da 400 da ake zargi, tare da kwato wasu daga cikin kayayyakin.

Advertisement

Sa’adatu Baba Ahmad wata mai amfani da kafar Sadarwa ta zamani ta wallafa labarin yadda ƴan Sanda suka afkawa unguwar Yakasai da Durumin Zungura a karamar hukumar Kano Munincipal domin kwato kayayyakin.

Ta rubuta “Tun da karfe 10 na safe ake kwato kayan da aka sace daga cikin gidajen mutanen da suka sace kadarorin Gwamnati da na waɗanda ba su ji ba ba su gani ba da sunan zanga-zanga, har zuwa yanzu Jami’an suna can suna bincike gidajen.”

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending