News
Najeriya Ba Ta Bukatar Mulkin Soja —Hamza Almustapha
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon shugaban jami’an tsaro na marigayi shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (rtd) ya yi kira da a inganta harkar aikin rundunar soji madadin juyin mulki kamar yadda aka goyi bayan yin hakan a wasu wurare.
Tsohon hafsan sojan ya na magana ne la’akari da kiraye-kirayen da wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa ke yi tare da ɗaga tutar ƙasar Rasha da nufin neman agajin ƙasashen waje.
Mun Kama ‘yanƙasar Poland bakwai a Kano kan ɗaga tutar Rasha a zanga-zanga – DSS
Helkwatar Tsaro ta yi gargaɗin cewa rundunar soji ba za ta karɓi duk wani kira da ya shafi juyin mulki ba, ta na mai cewa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen hukunta wani ko wasu da ke ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasa.
Al-Mustapha ya faɗi hakan ne a ya yayin hira da manema labarai a Abuja inda ya sanar da cewa “Ina mai gabatar da kai na yau a matsayin ɗan siyasa. Ina mai kallon ƙasar nan a yau ta fuskar demokraɗiyya. Mun zuba hannun jari a cikin sa, kuma mu na cigaba da zubawa a cikin sa. Duk bincikenmu ya ta’allaƙa ne a zuba hannun jari a demokraɗiyya mafi kyau a Nijeriya.”
Ya ce, duk da ba ya goyon salon tsarin mulkin da ƙasar ke tafiya a cikin ta, amma ya na so a samar da tsarin demokraɗiyya mai kyau ta yadda al’ummar ƙasa za su san ana mulki mai kyau, ya na mai bada misali da ƙasashen Birtaniya da Amurka.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
