News
TABARMAR KUNYA: Gwamnan Jihar Edo Godwin Obaseki Ya Yi Amai Ya Lashe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnan Jihar Edo ya yi amai ya lashe tabarmar kunyar sa, inda yanzu gwamnatin jihar ta ce gaskiya ta karɓi tirela 20 ta shinkafa daga hannun Gwamnantin Tarayya a kwanakin baya.
Hakan ya biyo bayan furucin da gwamnatin jihar ta fara yi ne kwanan baya ne inda Gwamna Godwin Obaseki ya ce bai karɓi ko buhu ɗaya ba.
Daliban Da Suka Kai Jami’ar Al-Qalam Kara, Sun Yi Nasara Kotu
Furta wannan iƙirari ke da wuya sai Ministan Harkokin Bunƙasa Yankin Neja Delta, Abubakar Momoh ya fito ya ce ƙarya Obaseki ke yi, an ba shi tireloli 20 na shinkafa daga gwamnatin tarayya.
To a yanzu dai jam’iyyar ce shinkafar da masu tarzoma suka daka wasoson ta a Benin babban birnin Jihar Edo, ta na daga cikin shinkafar da gwamnatin tarayya ta bai wa jihar, wadda Gwamnatin jihar ta ɓoye.
A wurin wani taron manema labarai a ranar Laraba a Benin, Kwamishinan Yaɗa Labarai Nehikhare ya tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Edo ta karɓi tireloli 20 na shinkafa daga gwamnatin tarayya.
Sai dai ya ce da aka kawo shinkafar, gwamnatin tarayya cewa ta yi a raba ta a sansanonin masu gudun hijira, gidajen marayu da ƙananan hukumomi.
Ya ce an bayar da shinkafar tun farkon wannan shekara ba kwanan nan ba.
Ya ce jihar Edo ba ta ɗauki ko buhu ɗaya ba, an raba ta duka inda gwamnatin tarayya ta ce a kai can a raba.
“Me shinkafa tirela 20 za ta magance wa jiha irin Edo mai mutum kusan miliyan bakwai?”
PREMIUM TIMES ta buga labarin da Minista Abubaks Momoh ya zargi cewa, ”Gwamnoni ke ƙara ƙaimin raɗaɗin tsadar rayuwa kan talakawa’.
A cikin zargin ya ce Gwamna Obaseki na Edo ya yi ƙarya da ya ce gwamnatin tarayya ba ta bai wa jihar tirelolin shinkafa 20 ba.
Ministan Bunƙasa Yankin Neja Delta, Abubakar Momoh, ya yi iƙirarin cewa rashin taɓuka ayyukan raya ƙasa da gina al’umma da wasu gwamnoni ke kasa yi ne ke ƙara ruruta raɗaɗin tsadar rayuwa ga al’ummar ƙasar nan.
Momoh ya yi wannan iƙirarin a ranar Talata, yayin da ya ke amsa tambayoyi a gidan talabijin na Channels TV da safe.
Ministan yana magana ne dangane da zanga-zangar da ke wakana a faɗin ƙasar nan, wadda ‘yan Najeriya ke yi saboda tsadar rayuwa.
Ya ce lallai tabbas akwai laifin gwamnoni a wannan matsalar, domin wasu gwamnoni ba su yin ayyukan raya jihohi da bunƙasa rayuwar jama’ar su, duk kuwa da maƙudan kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke danƙara masu a kowane wata.
“Na saurari musamman abin da matasa ke cewa, wai Gwamnatin Tarayya ba yin abin da ya wajaba sosai, wato abin da take yi bai wadatar ba.
“To amma bari na fito ɓaro-ɓaro. Ina jin yau a Najeriya daga lokacin da aka cire tallafin mai, ya kamata mutane su sani cewa ana danƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi kuɗaɗe. Kuma ana ba su kuɗaɗen don su yi wa jama’a abin da ya ce, ba don su sha shagalin gaban su da kuɗaɗen ba,” inji Momoh.
Momoh ya ce gwamnatin tarayya ta na bakin ƙoƙarin ta wajen ganin ta magance ko ta shawo kan matsalar tattalin arziki a ƙasar nan.
Daga nan Momoh ya ci gaba da lisafo irin ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ta yi kuma da waɗanda ta ke kan yi a faɗin ƙasar.
Sai dai kuma ya kare cire tallafin fetur da aka yi, wanda ya ce an yi ne domin a faɗaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
Momoh ya buga misali da yadda Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya ɓoye lodin shinkafa har cikin tireloli 20 waɗanda gwamnatin tarayya ta raba.
