Connect with us

News

Tsadar Rayuwa: An Gudanar Da Taron Addu’a A Faɗin Jihar Kano

Published

on

Addu'a
Gudanar da Sallah da addu'o'in a unguwanni daban-daban kamar su Na'ibawa, Hotoro, Fagge, Birged da sauran su

 

Duk da matsin lamba da kiran da aka dinga yi na dakatar da taron addu’a ta kasa kan halin matsin rayuwa da ake ciki a kasar nan, taron addu’ar ya gudana a ɓangarori da dama na jihar Kano.

Advertisement

DAILY NIGERAN HAUSA ta rawaito tun da fari an tsara gudanar da babban taron addu’ar a Masallacin Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi’u da ke unguwar Gwauron Dutse a Kano, sai dai daga bisani masu shirya taron su ka sanar da rarraba wuraren da za a yi sallar saboda dalilai na tsaro.

Malam Mubarak Ibrahim Lawal, ɗaya daga cikin masu shirya taron addu’ar a wani faifen bidiyo da ya wallafa ya ce an dakatar da gangamin ne bayan jami’an tsaro sun fada musu cewa ɓatagari na shirin farwa masu addu’ar.

Advertisement

Sai dai duk da wannan barazana da masu shirya taron suka fuskanta, an shirya tarukan addu’o’in a kananan hukumomi 44 na jihar.

Rahotanni na nuni da cewa  an gudanar da Sallah da addu’o’in a unguwanni daban-daban kamar su Na’ibawa, Hotoro, Fagge, Birged da sauran su.

Advertisement

Hakazalika wannan jarida ta gano cewa an gudanar da addu’o’in a masallatai da kuma wurare na sarari, inda taron ya samu halartar dumbin mutane a duk inda aka gudanar da shi.

Batun yin addu’ar ya samo asali ne daga zanga-zanga kan matsin rayuwa da aka fara 1 ga watan Agusta wacce bata gari suka shiga don dakile armashinta.

Advertisement

Hakan ne yasa masu zanga zangar suka zabi yin taron addu’o’i domin neman daukin Allah.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending