Connect with us

News

Ba Mu Sami Labarin Mutuwar Kowa Ba A Lokacin Zanga-Zanga – ‘Yan Sandan Kano

Published

on

Ba mu sami labarin utuwar kowa ba a lokacin Zanga Zanga – ‘yan sandan Kano

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kwamishinan yan sandan kano ya bayyana haka ne ranar Litinin a lokacin ganawarsa da ’yan jarida, inda ya ce rundunar ta kama mutane 873 kan laifin lalatawa da sace dukiyoyin jama’a da na gwamnati a lokacin zanga-zangar.

Advertisement

“A iya bayanan da muke da su, zuwa yanzu ba mu da rahoton asarar rai a yayin zanga-zangar,” in ji shi.

Gwamna Kano Abba Kabir Ya Janye Dokar Taƙaita Zirga-zirga Baki Ɗaya A Jihar 

Idan za a iya tunawa iyalan wasu matasa akalla uku da aka kashe a lokacin zanga-zangar, ciki har da wata budurwa da ake shirin daura aurenta.

Advertisement

Yan uwan wadanda aka kashe din, sun kuma yi zargin yan uwannasu sun rasu ne a sakamkon harbi daga jami’an tsaro, musamman ’yan sanda.

Iyalan wadanda suka rasun dai sun bayyana damuwa bisa yadda zanga-zangar da aka shirya ta lumana ta yi ajalinsu, inda suka bukaci a bi musu hakkinsu.

Advertisement

Zanga-zangar lumanar ta rikide zuwa tarzoma ne bayan da bata-gari suka kwace ta, suka rika fasa wurare suna sace-sace, tare da jikkata mutane a sassan jihar.

An yi dauki ba dadi tsakanin bata-garin da jami’an tsaro a kofar gidan gwamnatin jihar da sauran sassan jihar, inda aka kama sama da mutum 100.

Advertisement

Kazancewar lamarin ya kai ga gwamnatinn jihar, Abba Kabir, sanya dokar hana fita tsawon awa 24, kafin daga bisani a janye  dokar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending