Connect with us

News

Har yanzu Amurka na amfani da Jiragen Sama da Shekaru 34 yayin da Nigeria taki amfani da nata masu Shekaru 19

Published

on

1724184446298

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

A yayin da Shugaban Nigeria Bola Tinubu ya gaza amfani da Jiragen Sama masu Shekaru 19 sabida tsufa har yanzu Shugaban Kasar Amurka na amfani da jirgin sama da shekaru 34.

Advertisement

 

Wannan na zuwa ne bayan rashin cikakken bayani akan sayawa Shugaban Kasar sabon Jirgin Saman,kirar Airbus A330, a ranar Litinin din da ta gabata.

Advertisement

 

Tattauna batutuwa game da sabon jirgin shugaban kasar ya samo asali ne bayan matsalolin da jirgin Boeing Business Jet (BBJ) ya samu a zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo shekaru 19 da suka gabata inda ya samu matsala a wata tafiya da yayi Kasar Saudiyya da Netherlands da kuma Afirka ta Kudu.

Advertisement

 

Sai dai shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da jirgin saman haya, lamarin da fadar shugaban kasar ta bayyana a matsayin abin kunya ga Nigeria.

Advertisement

 

Yayin da jami’an gwamnati ke ta cece-ku-ce kan samar da wani sabon jirgin, talakawa sun nuna rashin amincewar su, ganin yadda matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da ke addabar Nijeriya.

Advertisement

 

Sai dai a watan Yuni, wata kafar yada labarai ta yanar gizo ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin Nijeriya ta sayi jirgin Airbus A330 daga wani bankin kasar Jamus.

Advertisement

Rahotanni sun bayyana cewa bankin ya kwace jirgin ne daga hannun wani basarake da ba a bayyana sunansa ba wanda ya ki biyan bashi.

Fadar shugaban kasar dai ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba, lamarin da ya bar jama’a cikin duhu game da sayan jirgin.

Advertisement

A yayin da ake ta cece-kuce a kan kamfanin saga na kasar Sin, ‘yan Nijeriya sun samu labarin cewa da gaske an sayi sabon jirgin. Amma duk da haka fadar shugaban kasar ta yi shiru har zuwa ranar Litinin lokacin da Bayo Onanuga, mataimaki na musamman ga Shugaban Kasa Bola Tinubu kan harkokin yada labarai, ya fitar da hotuna tare da bayanai.

 

Advertisement

Onanuga, wanda bai bayyana kudin sabon jirgin ba, ya ce, sabon jirgin da aka sayo bai yi wani tsada ba, kuma ya ceci Nijeriya da makudan kudaden da ake kashewa da kuma kudin man fetur.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending