Connect with us

News

Akwai Barazanar Fuskantar Ambaliyar Ruwan Sama A Kano –Hukumar  NiMet

Published

on

Jigawa Ambaliyar Ruwa Tayu Sanadiyar Mutuwar Mutane 16 Tare Lalata Gidaje 3,936 
Ambaliyar ruwan Sama

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet), ta yi gargaɗin samun ambaliya a wasu jihohin ƙasar sakamakon mamakon ruwan sama da za a samu kwanan nan.

Advertisement

Hukumar ta ce jihohin da suka haɗa da Kano, da Katsina, da Zamfara, da Jigawa da Kebbi da Kaduna, da kuma jihar Adamawa na cikin barazanar fuskantar ambaliyar ruwa, don haka ne ta yi kira ga mahukuntar jihohin su ɗauki matakan kare al’ummominsu.

Har yanzu Amurka na amfani da Jiragen Sama da Shekaru 34 yayin da Nigeria taki amfani da nata masu Shekaru 19

PRNigeria ta ruwaito cewa tuni dai dama ambaliyar ta fara ɓarna a wasu jihohin Najeriya inda aka samu asarar rayuka da ta dukiyoyi.

Advertisement

Alhaji Bashir Idris Garga, darakta a hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriyar NEMA ya ce wannan ruwan saman da za ayi na kwana uku ba ƙaƙautawa zai sanya magudanar ruwa da dama ba a cika damuwa da yashe su ba su cike wanda daga bisani ruwan zai malala har ya je yayi ɓarna.

“Saboda haka ya kamata a ɗauki mataki ƙwarai da gaske ya zama cewa ambaliyar bai yi ɓarna fiye da yadda ake zato ba.” daraktan ya ƙra da cewa.

Advertisement

Daraktan ya ce akwai irin wasu matakai da ake ɗauka na gaggawa irin su samun buhani a cika da yashi sai ayi tandagarƙi a canzawa ruwan akala yadda ba zai shiga yayi ɓarna ba.

Darakatan ya ƙara da cewa bayan haka, ya kamata a yashe magudanar ruwa sannan kuma a dage a sanar da ƴan uwa da abokan arziƙi cewa ga sanarwar da aka bayar kuma ya kamata a ɗau matakai.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending