News
Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano Ta Kama Manyan Jami’an Gwamnatin Jihar, Kan Badakalar Kudin Magungunan Kananan Hukumomi
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama manyan jami’an gwamnatin jihar, kan zargin badakalar kudin maganin kananan hukumomi
Cikin jami’an da hukumar ta kama sun hada da babban sakataran ma’aikatar kananan hukumomi Ibrahim Muhammad Kabara, da kuma shugaban karamar hukumar Tarauni, wanda shine shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ta kasa reshen jihar Kano (ALGON) Abdullahi Ibrahim Bashir, da Kuma wasu mutane biyar, da ake zarginsu da hannu a badakalar kwangilar magungunan kananan hukumomi 44.
Akwai Barazanar Fuskantar Ambaliyar Ruwan Sama A Kano –Hukumar NiMet
Kazalika hukumar ta aike da takardar gaiyata ga shugaban rukunin shagunan magani na NOVEMED, wanda ‘da ne wurin tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.
Hukumar na tuhumar wadannan mutane da sabawa dokokin tsarin aikin gwamnati, ta hanyar aiwatar da kwangilar da bata cika ka’ida ba, ba tare kuma da sahalewar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ba.
Jaridar Solacebase ta rawaito wata majiya na cewa, tuni shugaban ALGON Kuma shugaban karamar hukumar Tarauni, ya amsa laifin sa, Inda ya tabbatar da cewa, ya bayarda da umarni ba bisa ka’ida ba, na biyan sama da naira millyan 402 cikin kudaden siyan magunguna ga kananan hukumomin jihar.
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
