News
Zaben Kananan Hukumomi A Kano: Babu Gudu Ba Jada Baya Akan Miliyan 10 Da Miliyan 5 A Matsayin Kudin Tsayawa Takarar Chairman Da Kansila —KANSIEC
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC, ta ce ba gudu ba ja da baya kan kudaden tsayawa takarar shugabancin kananan hukumomi da kansiloli a jihar.
Hukumar dai ta sanya Naira miliyan 10 ga duk wanda ke son tsayawa takarar shugabancin karamar hukuma da kuma Naira miliyan 5 ga kansila.
Rahotanni na nuni da cewa sanya kudaden dai ya janyo suka daga jam’iyyun adawa wadan suka bayyana matakin a matsayin yunkurin hana su tsayawa takara.
Sai dai shugaban hukumar zaben Parfesa Sani Lawan Malumfashi, ya yi watsi da karafen-korafen, ya na mai cewa ba gudu ba ja da baya.
Akan sanya Naira miliyan 10 ga duk wanda ke son tsayawa takarar shugabancin karamar hukuma da kuma Naira miliyan 5 ga kansila.
NAN
-
News2 days ago
Shettima @60: Haƙurinsa, Biyayyarsa Sun Taimaka Wajen Ciyar Da Manufofin Shugaba Tinubu Gaba — Kwankwaso
-
News5 days ago
KANO:’Yan Mata Uku ’Yan Gida Ɗaya Sun Mutu A Kifewar kwale-kwale A Tiga
-
News5 days ago
Kwamitin Tsara Kundin Yakin Neman Zaɓen Gwamnan Kano Ya Yi Taron Tsare-tsare Manufofin Ci Gaban Jihar A Kaduna
