News
Wasu Matasa Sun Fatattaki Dan Majalissar Tarayya Ya Yi Jana’izar Sarkin Ningi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu fusatattun matasa sun kai hari ga dan majalisar wakilai mai wakiltar Mazabar Ningi/Warji a Jihar Bauchi, Hon. Adamu Hashimu Ranga, a wajen jana’izar marigayi Sarkin Ningi.
WIKKI TIMES ta ruwaito cewa Sarkin Ningi, Alh. Yunusa Mohammed Danyaya, ya rasu a daren Asabar kuma anyi Jana’izar sa a masarautarsa a Ningi a ranar Lahadi.
Bayan Dawowa Daga Faransa Shugaba Tinubu Zai Kai Ziyara China
Rahotanni na nuni da cewa Hon. Ranga yaje Ningi ne domin halartar sallar jana’izar basaraken.
Sai dai wasu matasa a mazabar sun nuna rashin jin dadinsu kan cewa dan majalisar ba ya wakiltarsu yadda ya kamata a majalisar wakilai.
Lamarin ya faru ne a fadar Sarkin Ningi jim kadan bayan an kammala sallar jana’iza, yayin da dan majalisar ke shirin barin wurin.
Wasu ganau sun ce lokacin da Hon. Ranga yake barin fadar da misalin karfe 5:42 na yamma, wasu gungun matasa sun fara ihun “Ba ma yi, ba ma yi” tare da watsa masa kasa da jifan sa da duwatsu.
Wakilinmu da ke wurin ya lura cewa harin ya tsananta yayin da dan majalisar ke tafiya zuwa motarsa. Lamarin da ya haifar da fasa gilasai da madubin motar Dan majalissar.
Wani shaidan gani da ido, Munkaila Salisu, ya bayyana lamarin a matsayin abin bakin ciki, “Na fito daga fadar sarkin cike da damuwa kan rasuwar sarkin, sai kawai na ji ihun matasa suna jifa da kasa da duwatsu.
Da na matsa kusa, sai na fahimci cewa wakilinmu ake kaiwa hari. Ba zan iya tabbatar da ko an ji masa rauni ba, amma gilasai da madubin motar sun lalace,” inji shi.
Kokarin WikkiTimes na tuntubar Hon. Ranga don jin ta bakinsa abin yaci tura, domin bai dauki waya ba kuma bai amsa sakon da aka tura masa ba.
Sai dai WikkiTimes ta samu labarin cewa dan majalisar ya koma Ningi ranar Litinin tare da rakiyar jami’an tsaro domin bashi Kariya yayin da yaje ta’aziyya
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
