Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya ta amince da Naira N3.5bn ga hukumar Kula da Ilimin bai daya ta UBEC domin Kara inganta Ilimi a Nigeria 

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnati Tarayya ta amince da kara yawan kudaden tallafin da ya dace na tsarin ilimi na bai daya da gwamnatocin jihohi za su samu domin gudanar da ayyukan more rayuwa.

Sakataren zartarwa na hukumar kula da ilimin bai daya ta kasa Hamid Bobboyi shine ya sanar da hakan a wani taron horarwa da hukumar ta shiryawa shuwagabannin hukumar ta (SUBEB) da sakatarorin hukumar na tsawon kwanaki biyar a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Advertisement

 

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na UBEC, David Apeh, ya fitar, ta ruwaito sakataren zartarwa na cewa, karin tallafin da ake baiwa jihohi don aiwatar da ayyuka ya fito ne daga kashi 2% na asusun tattara kudaden shiga da aka ware domin tallafa wa ilimi a Najeriya.

Advertisement

 

Bobboyi ya bayyana cewa amincewar ta biyo bayan daftarin kasafin kudin shekarar 2024 da kuma amincewa da hakan a matsayain doka.

Advertisement

Ya ce Kudin da gwamnatin tarayya ta bayar na shekarar 2024 na tallafin da ya dace da UBEC ga kowace jiha shine N3,554,642,584.46.

Ya ce Taimakon ya bi sashe na 11 (2) na dokar UBEC na shekarar 2004, yayin da ake bukatar gwamnatocin jihohi su samar da kwatankwacin adadin N3,554,642,584.46 a matsayin wani asusun takwararta don aiwatar da ayyukan shiga ga hukumar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending