Connect with us

News

Annobar Ambaliyar Ruwa ta Raba Mutane 1,000 da Muhallansu a Kafanchan, Sauran Sassan Yankin

Published

on

Jigawa Ambaliyar Ruwa Tayu Sanadiyar Mutuwar Mutane 16 Tare Lalata Gidaje 3,936 

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Wata mummunar annobar ambaliyar ruwa ta raba sama da mutane dubu daya da muhallansu, tare da yin sanadiyyar mutuwar kananan yara biyu a yankin Kafanchan, dama sassan kauyukan karamar hukumar Jema’a ta jihar Kaduna.

Advertisement

Mataimakiyar shugaban karamar hukumar ta Jema’a Misis Christy Usman ce ta bayyana hakan, jim kadan bayan ziyarar gani da da ta kai da tawagar jami’ai dake duba matsalar da ambaliyar ta haifar a yankin kudancin jihar.

AMBALIYAR RUWA: Sama Da Fursunoni 200 Sun Tsere Daga Gidan Yarin Maiduguri

Tace annobar ambaliyar da ta lakume yankin garin Kafanchan da Jagindi da Aso da kuma Bade, ta lalata gonaki da dama da kuma amfanin gona na dubban milyoyi.

Advertisement

“Wannan annoba ta taba tattalin arzikin wadannan yankunan na karamar hukumar Jema’a, sai dai muna godiya ga Gwamna Uba Sani da tuni ya turo da jami’ai don duba asarar da aka samu karkashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar Gwamnati Malam Sani Liman Kila.

Ta bayyana kwarin gwiwarta kan cewa Gwamnatin jihar ta Kaduna za tayi tsari don tallafawa wadanda asarar ta shafa.

Advertisement

“Yara biyu ne ambaliyar ta tafi da su cikin magudanar ruwa a Kafanchan”, cewar Usman.

Bayan kewaya sauran sassan da annobar ambaliyar ta shafa a Sanga, Jema’a da kuma Kachia, Malam Sani Liman Kila ya bayyana cewa mutanen yankin na bukatar agajin gaggawa don farfadowa daga wannan matsalar.

Advertisement

Ya kara da cewa, ambaliyar ta kuma lalata gadar kananan hukumomin Agom da kuma, dake hada al’ummar yankuna biyar dake yankin tare da rusa gidaje a Nandu.

Jami’an sun kuma alakanta faruwar hakan da toshewar magudanan ruwa da yin ginin akan su, inda ya ce kwamitin su zai mika rahotonsa ga Gwamnan jihar don neman agajin gaggawa daga hukumar NEMA.

Advertisement

A gefe guda, wadanda ambaliyar Ruwan ta shafa sun bayyana rashin jin dadinsu ganin yadda annobar ke faruwa duk shekara.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending