News
Ambaliyar Ruwan : Nan Da Sati Biyu Zamu Tabbatar Da Kowa Ya Koma Muhallinsa _ Kashim Shattima
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ziyarci birnin Maiduguri a jiya Talata domin jajantawa mutanen Borno wanda ambaliyar ruwa ya shafa.
Shettima wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa birnin ya samu tarba daga Gwamna Farfesa Babagana Zulum, wanda ya raka shi fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar El-Kanemi inda ambaliyar ruwan tafi kamari.
mataimakin shugaban kasar ya ziyarci sansanin Bakassi inda dubban mutane ke zaman gudun hijira.
Shettima ya shaidawa mutanen da lamarin ya shafa cewa, gwamnati za ta basu tallafin shinkafa Tirela 50.
Ya kara da cewa, gwamnatin za ta hada kai da hukumar raya yankin arewa maso gabas don tabbatar da cewa mutanen basu wuce makwanni 2 a sansanin ba.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa, ambaliyar ruwa ta afkawa garin Maiduguri inda ta tafi da gidaje da hanyoyi da dama.
