News
Shugaba Tinubu Ya Yaba Da Ayyukan Sojojin Arewacin Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba Kasa Bola Tinubu ya nuna Jin daɗinsa na labarin nasarorin da sojojin suke samu na yaƙi da masuyiwa Kasa barazanar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya.
Cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce Tinubu Ya yaba da irin ayyuka da jami’an tsaron sukeyi na bada tabbaci ga zaman lafiya da tsaro ga al’umma Najeriya.
Dakarun Operation Hadarin Daji, a ranar Alhamis, sun yi nasarar kashe wani shugaban ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo mai Suna , Halilu Sububu, wanda ya addabi al’umma a yankunan Zamfara, Sokoto, da sauran sassan arewa maso yammacin Najeriya.
Sa’annan Sojojin sun kuma kashe wani dan ta’adda shima mai suna Sani Wala Burki a wani aikin hadin gwiwa da Sojijin suka kai a Katsina, tare da tarwatsa wani yanki na ‘yan ta’adda a Kaduna, inda aka sako dalibai 13 da yan bindingar sukayi garkuwa da su.
Wadannan nasarori da sojojin suka sumu ya biyo bayan umarnin da Shugaban kasa ya bayar na kawadda ta,addanci a Najeriya da kuma kwarin gwiwa da shugaban hafsoshin tsaro Christopher Musa ya bayar na bada tabbaci akan dakile ayyukan yan bindingar.
Shugaba Tinubu ya kuma yabawa babban hafsan soji, hukumomin leken asiri, da sojoji bisa jajircewarsu da hadin kai, da sadaukarwa, wanda ya haifar da kyakkyawan sakamako a baya-bayan nan.
Shugaban ya kuma yabawa jami’an tsaro baki daya kan inganta tsaro a kasar nan, inda ya kuma umurce su da su ci gaba da kokari har sai an kawar da barazanar ta,addanci a fading Najeriya.
Shugaba Tinubu ya tabbatar wa jami’an tsaro goyon bayansa na ci gaba da cim ma burin da aka sa a gaba na tabbatar da tsaron al’umma.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
