Connect with us

News

Kotun Saudiyya Ta Yanke Wa Tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasar Ɗaurin Shekara 20

Published

on

Kotun Saudiyya Ta Yanke Wa Tsohon Babban Hafsan Tsaron Ƙasar Ɗaurin Shekara 20
Janar Khalid Bin Qarar al-Harbi, ya jagoranci hukumar tsaro ƙasar na tsawon shekara shida

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Kotu a Saudiyya ta yanke hukuncin ɗaurin shekara 20 a kan tsohon shugaban harkokin tsaron ƙasar kan laifukan Rashawa.

Haka kuma kotun ta ci tarar Janar Khalid Bin Qarar al-Harbi, dala 250,000 tare da umartarsa ya maido da kuɗaɗen da suka kai dala miliyan 3.5 na rashawa da ya wawushe.

Kamfanin NNPCL Zai Fara Lodin Man Fetur Daga Matatar Dangote Ranar 15 Ga Satumba

An samu tsohon jami’in – da ya riƙe wannan muƙami a ma’aikatar tsaro na tsawon shekara shida – da laifukan zamba da karɓar kuɗaɗen tsohiya da amfani da muƙaminsa wajen biyan buƙatun kansa.

BBC ta ruwaito cewa Hukuncin shi ne na ƙarshe kuma babu damar daukaka kara. Ma’aikatar cikin gida ta ƙasar ta jaddada udurin gwamnatin ƙasar na ci gaba da yaƙi da duk wani nau’in cin hanci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending