Connect with us

News

Shugaba Tinubu Ya Yaba Da Ayyukan Sojojin Arewacin Najeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaba Kasa Bola Tinubu ya nuna Jin daɗinsa na labarin nasarorin da sojojin  suke samu na yaƙi da masuyiwa Kasa barazanar tsaro a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

 

Advertisement

Cikin wata sanarwar da mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar ya ce Tinubu Ya yaba da irin ayyuka da jami’an tsaron sukeyi na bada tabbaci ga zaman lafiya da tsaro ga al’umma Najeriya.

 

Advertisement

Dakarun Operation Hadarin Daji, a ranar Alhamis, sun yi nasarar kashe wani shugaban ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo mai Suna , Halilu Sububu, wanda ya addabi al’umma a yankunan Zamfara, Sokoto, da sauran sassan arewa maso yammacin Najeriya.

 

Advertisement

Sa’annan Sojojin sun kuma kashe wani dan ta’adda shima mai suna Sani Wala Burki a wani aikin hadin gwiwa da  Sojijin suka kai a Katsina, tare da tarwatsa wani yanki na ‘yan ta’adda a Kaduna, inda aka sako dalibai 13 da yan bindingar sukayi garkuwa da su.

 

Advertisement

Wadannan nasarori da sojojin suka sumu ya biyo bayan umarnin da Shugaban kasa ya bayar na kawadda ta,addanci a Najeriya da kuma kwarin gwiwa da shugaban hafsoshin tsaro Christopher Musa ya bayar na bada tabbaci akan dakile ayyukan yan bindingar.

 

Advertisement

Shugaba Tinubu ya kuma yabawa babban hafsan soji, hukumomin leken asiri, da sojoji bisa jajircewarsu da hadin kai, da sadaukarwa, wanda ya haifar da kyakkyawan sakamako a baya-bayan nan.

Shugaban ya kuma yabawa jami’an tsaro baki daya kan inganta tsaro a kasar nan, inda ya kuma umurce su da su ci gaba da kokari har sai an kawar da barazanar ta,addanci a fading Najeriya.

Advertisement

Shugaba Tinubu ya tabbatar wa jami’an tsaro goyon bayansa na ci gaba da cim ma burin da aka sa a gaba na tabbatar da tsaron al’umma.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending