News
Kotu Ta Sanya Ranar Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masarautar Nassarawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata babbar kotun jihar Kano, ta sanya ranar 10 ga Oktoba 2024, don yanke hukunci kan karar da aka shigar gabanta na neman hana mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado-Bayero gyaran gidan sarki na Nassarawa.
Gwamnatin Jihar Kano da Babban Lauyan Kano da kuma Majalisar Masarautar Kano ne , suka shigar da karar ta hannun lauyansu Rilwanu Umar SAN, wanda ya shigar da karar a ranar 12 ga Satumba 2024.
Masu karar na neman kotu ta hana Alhaji Aminu Ado-Bayero gyara gidan sarki na Nasarawa da ke kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar Kano.
A lokacin da ake sauraron karar, Lauyan ma su kara Habib Akilu, ya shaida wa kotun cewa wanda ake karar ko shi ko wakilansa ba wanda ya halarci zaman kotun.
Akilu ya gabatar da takardar neman shiga tsakani yana neman a hana wanda ake kara sake ginawa ko canza fasalin gidan sarkin na Nasarawa.
Daily Trust ta rawaito cewa a ranar 13 ga watan Satumba 2024, kotun ta bayar da umarnin dakatar da wanda ake kara, da wakilansa, daga rushewa, gyarawa, ko sake gina gidan Sarkin na Nasarawa da ke kan titin zuwa gidan gwamnatin jihar Kano, har zuwa lokacin da za a saurari karar da kuma yanke hukunci a kan Shari’ar.
Kotun ta kuma umurci dukkanin bangarorin da suke cikin karar da su tsaya a yadda suke har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.
-
News6 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News5 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News6 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

