Politics
RIKICIN SHUGABANCI : Tababa Da Rashin Tabbas Sun Mamaye Jam’iyyar PDP
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga rudani dangane da shugabannin dake jagorancin ta sakamakon rahotan korar da shugaban riko Iliya Damagum da Sakataren ta Samuel Anyawu da aka ruwaito kwamitin gudanarwa na kasa ya yi.
DAILY TRUST ta ruwaito cewa yayin da ake wannan sai kuma bangaren Damagum ya sanar da dakatar da Sakataren yada labaran jam’iyyar ta kasa Debo Olugunagba da Mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a Kamaldeen Adeyemi Ajibade.
Tuni wannan mataki ya sake farraka kan yayan jam’iyyar wadda ta dade tana fama da rikicin cikin gidan da ya hana ta tasiri a zaben shugaban kasar da akayi bara.
Rahotanni sun ce bangarorin sun ruga kotu, ya yin da wasu daga cikin jiga jigan jam’iyyar suka fara tintibar juna domin samo hanyar da za su dinke barakar da aka samu. A halin yanzu dai ana samun tababa dangane da sahihan shugabannin dake jagorancin jam’iyyar wadda ta kwashe shekaru 16 a karagar mulkin Najeriya.
