Politics
Jam’iyyar APC ta gana da Akpabio da sauran sanatoci kan batun shugaban majalisa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A wani ɓangare na yunƙurin da kwamitin gudanarwar jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke yi na ganin ta magance matsalolin da jam’iyyar ke fuskanta kan shugabancin majalisun dokokin ƙasar, jam’iyyar ta gana da Sanata Godswill Akpabio da Sanata Jibrin Barau, da kuma wasu sanatocin
A wani saƙo da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce ta gana da zaɓaɓɓun sanatoci na jam’iyyar da sauran jam’iyyu domin nuna goyon bayansu ga zaɓin kwamitin gudanarwar jam’iyyar kan batun shugabancin majalisar.
APC dai ta nuna goyon bayanta ga Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa, sai kuma Sanata Jibrin Barau a matsayin mataimaki, matakin da bai yi wa wasu daga cikin sanatocin daɗi ba, lamarin da har yanzu ke tayar da jijiyar wuya tsakanin ‘yan majalisar da ke sha’awar ɗarewa kujerar.
Jam’iyyar ta ce ta gana da sanatocin ne domin tuntuɓar shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu wanda ke jagorantar kwamitin gudanarwar jam’iyyar.
Sanata Akpabio da Sanata Jibrin Barau tare da sauran sanatoci kimanin 40 sun hallara a wajen ganawar da aka gudanar a Abuja babban birnin ƙasar ranar Talata.
A ƙarshen ganawar, wadda aka gudanar a asirce, Sanata Akpabio ya bayyana jin daɗinsa na wanda zai kasance sabon shugaban majalisar dattawa mai zuwa.
