Politics
Kwankwasiyya Na Fuskantar Rikici: Zan Bayyana Gaskiyar Kalar Jibrin Kofa – Aliyu Madaki

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan majalisar wakilai Aliyu Sani Madaki mai wakiltar karamar hukumar Dala a majalisar wakilai ta kasa a karkashin jam’iyyar (NNPP), ya bayyana ra’ayinsa game da abokin aikinsa Abdulmumini Jibrin Kofa mai wakiltar mazabar Bebeji da Kiru na tarayya.
A wani tsokaci da ya wallafa a shafin sa na Facebook MADAKI kamar yanda Jaridar KANO TIMES ta ruwaito
MATASA: Duk Da Wannan Tsadar Rayuwa Da Kuke Sha Amma Kun Kasa Fitowa Kuyi Bore — Tsohon Minista
“Al’ummar Jihar Kano da Nijeriya, a yau zan gaya muku wanene Abdulmumini Jibrin da kuma wane ne Aliyu Sani Madaki. Tunda shi mutum ne marar kunya, a yau zan bayyana abin da muka tattauna da kuma abin da ya ce game da Kwankwaso,” in ji Madaki, wanda ya janyo cece-kuce a fagen siyasar yankin.
Dukkan ‘yan siyasar biyu ana daukarsu a matsayin ginshikan tafiyar Kwankwasiyya a jihar Kano, akidar siyasar tsohon gwamna Rabiu Kwankwaso ya kafa.
Kalaman Madaki sun tayar da kura tare da kara tada jijiyoyin wuya game da daidaiton kawance a cikin tafiyar Kwankwasiyya, yayin da ake ganin adawar siyasa na kara kamari gabanin zabe mai zuwa.
Masu lura da al’amura dai na ganin cewa irin wannan rashin jituwa na iya yin tasiri ga hadin kan jam’iyya da kuma ra’ayin masu zabe a jihar Kano.