Politics
ZABEN KANANAN HUKUMONI: Jam’iyyar APP Ta Lashe Kujeru 22 Cikin 23 A Ribas

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jam’iyyar Action People’s Party (APP) ta lashe kujeru 22 daga cikin 23 a zaben kananan hukumomi da aka kammala a jihar Ribas.
Babban Jami’in Zabe na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Ribas (RSIEC) Adolphus Enebeli ya bayyana sakamakon zaben a Yau ranar Asabar a Fatakwal.
Sai dai alkalan zaben jihar sun dakatar da bayyana sakamakon karamar hukumar Etche (LGA) saboda ana ci gaba da tattara sakamakon zaben.
Enebeli ya ce za a bayyana sakamakon karamar hukumar Etche tare da na kujerun kansiloli 319 a nan gaba.
Idan ba’a manta gwamna Fubura na Jihar ta Ribas shine ya bayar Da Umarni Ga ‘yan Takarar Kananan Hukumomin Domin tsayawa Takara a Jam’iyyar APP Bayan Da tsohon gwamnan Jihar Nyesom Wike ya kwace Ragamar Jam’iyyar PDP a kotu.
Sai gwamna Fubura ya Yi zargin Rundunar Yan Sandan Nageriya Da Anfani Da bakin wuta Domin taimakawa PDP tsagin Wike.