News
Bawa Hon. Yusif Ata muƙamin ministan gidaje da shugaban ƙasa ya yi, ya ɗora ƙwarya a gurbin ta – Amb. Ƙaribu Kabara.
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta ce muƙamin da shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tunibu ya bai wa Honarable Yusuf Abdullahi Ata, matsayin ministan gidaje ya dora ƙwarya a gurbin ta.
Babban daraktan ƙungiyar a Najeriya Ambasada Ƙabiru Yahaya Lawal Kabara ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai a ranar Lahadi, ya ce kasancewar Honarable Yusuf Ata Fagge mutum ne da ke da kishin al’umma, a don haka ne suke da yaƙinin zai kawo wa al’umma ci gaba a ɓangarori daban-daban a Najeriya.
“Bai wa Honarable Yusuf Ata Fagge, matsayin ministan gidaje an yi wa al’ummar jihar Kano gata, kuma muna kyautata zaton zai riƙe amanar da aka bashi tare da samar da ci gaban al’umma da ma na gwamnatin tarayya, “in ji Amb. Ƙaribu”.
Kabara ya kuma yi kira ga sabon ministan na gidaje Hon. Ata Fagge da ya ƙara himma wajen rike amana tare da kula da kowa da kuma cire ɓangarancin siyasa kamar yadda yake a baya, domin samar da ci gaban Jama’a.
Daga ƙarshe Ƙaribu Kabara ya kuma taya ministan murna kan muƙamin ministan gidaje da shugaban ƙasa Tinubu ya bashi, inda ya kuma yi addu’ar Allah ya taya Honarable Yusuf Abdullahi Ata Fagge, da cewar Allah ya taya shi riƙo ya bashi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa.
