News
Farashin Buhun Gawayi Ya Kara Yin Tashin Gwauron Zabi A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Mazauna Birnin Kano sun koka kan yadda sukace farashin gawayi ya sakeyin tashin gwauron zabi a wannan lokacin.
A halin yanzu farashin dauri daya ya tashi zuwa N300, daga N200 da ake sayar da shi a makonnin uku
Gurfanar Da Yara Ƙanana A Gaban Kotu Abun Kunya Ne Ga Dimokradiyya Najeriya –Shehu Sani
Buhun gawayin kuma ya tashi daga 6300 ya koma Naira 8,500 zuwa 9,000 akan sarin kowanne buhun guda saboda yawan amfani da shi da kuma Matsalar wutar Lantarki da aka samu a Arewacin Najeriya.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa an samu karuwar yadda mutane ke yin tururuwar amfani da gawayin a wurare daban-daban sakamakon tsadar farashin gas.
Wani mai sayar gawayi a unguwar Tudun Yola dake Kano, Malam Sani Umar ya ce cewa tsananin tsadar rayuwa ya sa mutane jinginar da tukwanen iskar gas ɗin su na girki sun rungumi girki da gawayi a wannan Lokacin.
Malam Umar Mai gawayi ya Kara alakanta tashin gawayin da matsalar rashin wutar lantarki da aka samu a Arewacin Najeriya inda aka samu kirin Naira 2,500 a duk buhu.
Haka zalika Wani dan kasuwa dake kano ya ce iyalinsa na amfani da gawayi yanzu saboda yawansu ba zai iya jure siyar Gas ba a wannan lokaci da ake ciki.
