Connect with us

News

Gwamnatin Bauchi Ta Dakatar Da Ma’aikata 6 Bisa Zargin Sayar Da Kadarorin Gwamnati

Published

on

Gwamnatin Bauchi Ta Dakatar Da Ma’aikata 6 Kan Zargin Sayar Da Kadarorin Gwamnati

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar kula da aikin gwamnati ta Jihar Bauchi ta dakatar da wasu ma’aikata shida daga ma’aikatar ayyuka da sufuri bisa zargin karkatar da kadarorin gwamnati da ke karkashin kulawarsu.

Advertisement

Ana zargin ma’aikata da sayar da kayan aikin da aka cire daga wuraren aikin gadar sama a Wunti da kasuwar Central da ke Bauchi, wanda darajarsu ta kai miliyoyin naira.

Dan Makaranta Ya Daba Wa Mutane 25 Wuka Saboda Ya Fadi Jarrabawa

Ma’aikatan da aka dakatar da su, wadanda ke aiki tare da Hukumar Rayaw da Kula da Kayayyakin Aikin Gine-Gine ta Jiha (BASIDMA), an ce sun aikata laifin da ya saba wa Sashe na 0327 na dokokin aikin gwamnati na Jihar Bauchi.

Advertisement

Sanarwar da Sale Umar, jami’in hulda da jama’a na hukumar, ya sanya wa hannu ta bayyana sunayen wadanda abin ya shafa wanda ya hada da Mohammed Musa Saye, Babban Jami’in Ajiya, Ado Abba Pali, Babban Jami’in Fasaha, Danladi Noma, Babban Jami’in Wuta, Garba Nuhu, Babban Jami’in Ayyuka, Ibrahim Inuwa, Mataimakin Kwararren Injiniya na Lantarki, da Uzairu Mudi, wanda shi ma Mataimakin Kwararren Injiniya na Lantarki ne.

Sanarwar ta ce hukumar ta yi aiki ne bisa tanadin Sashe na 0331 na dokokin aikin gwamnati na Jihar Bauchi, inda ta amince da dakatar da ma’aikatan domin baiwa hukumomin da suka dace damar bincike kan zargin da ake musu.

Advertisement

“An zargi ma’aikatan da dakatarwar ta shafa da sayarwa ko kuma karkatar da kadarorin gwamnati da aka cire daga wuraren aikin gada a Wunti da kasuwar Central da ke Bauchi, wanda ya saba wa Sashe na 0327 na dokokin aikin gwamnati na jihar Bauchi,” in ji sanarwar.

Haka zalika, hukumar ta ce ta yi la’akari da wata kara da wani babban ma’aikacin Gidan Rediyon Bauchi (BRC) ya gabatar, inda ya ce an ware shi daga cikin jerin ma’aikatan da aka bayar da sunayensu don karin girma.

Advertisement

“Hukumar kula da gidan rediyon Bauchi ta umarci hukumar gudanarwar gidan rediyon da su sake gabatar da sahihin jerin sunayen ma’aikatan da suka cancanci karin girma, ciki har da Bashir Idris wanda aka ware daga jerin ma’aikatan,” sanarwar ta kara.

Za’a tuna cewa, a watan Satumba da ya gabata, hukumar ta dakatar da sakatarorin dindindin uku daga ofishin sakataren gwamnatin jiha, ma’aikatar ilimi mai zurfi, da ma’aikatar albarkatun kasa bisa zargin aikata manyan laifuka.

Advertisement

 

WIKKI TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending