News
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya amince da dawo da ma’aikata 9,332 da aka Dakatar a watannin baya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf ya amince da dawo da ma’aikata 9,332 da aka Dakatar a watannin baya
Matakin dawo da ma’aikatan ya Biyo Bayan Kammala Tantance wa da Kwamitin da Gwamnan Jihar Kano ya kafa ya Kuma Mika Rahotansa
Kano: ‘Yan sanda sun gargadi jam’iyyar NNPP da APC kan zanga-zangar da suka shirya yi ranar Asabar
Idan za a tuna dai tsohon Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya Dauki ma’aikatan yana daf da kammala mulkinsa, Yayinda Kuma Abba Kabir Yusuf ya Dakatar Dasu Yana Mai cewa Sai an Tantance su.
Sanarwar da Ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Kano Dr baffa Bichi ya Fitar yau Juma’a ta Bayyana Mayar da wadannan ma’aikatan da suka Kai 9,332
Jaridar Inda Ranka Ta Rawaito cewa Akalla ma’aikatan sun Kai 11,500 to sai Dai Kuma Daga Cikinsu Dubu 9,332 ne suka Tsallake Tantancewar da Akayi musu
