Connect with us

News

Kano: ‘Yan sanda sun gargadi jam’iyyar NNPP da APC kan zanga-zangar da suka shirya yi ranar Asabar

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi jam’iyya mai mulki ta New Nigeria People Party (NNPP) da jam’iyyar adawa ta APC da su janye zanga-zangar da aka shirya yi ranar Asabar.

Rundunar ‘yan sandan ta yi barazanar za ta yi rashin tausayi, tare da duk wanda aka kama a yayin gudanar da zanga-zangar a jihar.

Advertisement

Idan dai ba a manta ba jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa jam’iyyun NNPP da APC ne suka hada magoya bayansu domin shirya zanga-zanga a ranar Asabar.

Domin bayyana ra’ayoyinsu kan hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke a baya-bayan nan, wadda ta ayyana hukunce-hukunce masu cike da cece-kuce kan zaben gwamna.

Advertisement

A halin da ake ciki kuma, matakin da bangarorin biyu suka dauka tun bayan sanarwar, ya haifar da fargaba a zukatan mazauna jihar kano yadda irin wannan zanga-zangar da aka gudanar a wannan rana na iya haifar da wahalhalu da hargitsi ga  al’ummar jihar.

Sai dai a wata sanarwa da ya sanya wa hannu a madadin kwamishinan ‘yan sandan jihar Mista Husaini Gumel, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO) SP. Haruna Kiyawa ya gabatar wa manema labarai a ranar Juma’a;

Advertisement

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Sahihan bayanai da rundunar ta samu sun nuna cewa wasu gungun mutane da ke ikirarin magoya bayan jam’iyyar NNPP da APC ne ke amfani da kafafen yada labarai daban-daban tare da jan hankalin jama’a tare da shirin shiga tituna a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba 2023 domin gudanar da zanga-zangara adawa da hukuncin da kotun daukaka kara ta jihar Kano ta yanke.”

Ya kara da cewa, “Bayanan sun kuma nuna cewa manufar masu zanga-zangar ita ce rufe jihar da kuma kaiwa fitattun ‘yan adawar jam’iyyar siyasa hari; matakin da zai iya haifar da tashin hankali.”

Advertisement

 

“A halin da ake ciki, rundunar ‘yan sandan ta bayyana karara cewa kamar yadda ba a samu wata sanarwa ta hukuma daga wata jam’iyyar siyasa ba game da shirin gudanar da wata zanga-zanga ko taro.”

Advertisement

 

Rundunar ‘yan sandan ta yi wannan gargadi ne ga daukacin mazauna jihar da su yi taka-tsan-tsan domin duk wanda ya yi niyyar gudanar da wata zanga-zanga ko muzahara ya yi hakan ne kawai bisa tanadin doka.

Advertisement

Idan  za ku tuna cewa gabanin da kuma bayan hukuncin kotun daukaka kara ta gwamnan jihar Kano, shugabannin jam’iyyun NNPP da APC sun halarci tare da rattaba hannu kan wata yarjejeniya a tsakaninsu a gaban rundunar ‘yan sandan jihar Kano,

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending