News
YANZU-YANZU: Hukumar EFCC Ta Gurfanar Da Yahya Bello gaban kotu a abuja kan zargin wawushe Naira Biliyan 80
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, an gurfanar da shi a Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Maitama, Abuja, ta hannun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta (EFCC).
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa EFCC ta ayyana Yahaya Bello a matsayin wanda ake nema bayan ya kasa amsa gayyata da dama da aka yi masa kafin a fara yi masa shari’a ba tare da halartar kotu ba.
Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra’ila Da Hezbollah Ta Fara Aiki A Lebanon
Jami’an hukumar sun bayyanawa Daily TRUST cewa an kama Bello ta hanyar dabaru da ‘yan sanda na musamman suka yi amfani da su, sabanin rahotannin da ke cewa ya kai kansa ofishin EFCC.
Tsohon gwamnan ya shiga cikin wata babbar shari’ar almundahana, inda EFCC ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema tun ranar 18 ga Afrilu, 2024, dangane da tuhumar almundahanar Naira biliyan 80.2.
An gurfanar da sabbin tuhume-tuhume a kan tsohon gwamnan gaban Mai Shari’a Maryanne Anenih na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Maitama, Abuja.
A zaman kotun da aka yi ranar 14 ga Nuwamba, an dage shari’ar zuwa yau (27 ga Nuwamba), bayan lauyan EFCC ya nemi a dage shari’ar sabbin tuhume-tuhumen da aka yi wa Bello.
EFCC ta ce wa’adin kwanaki 30 da aka bai wa Bello bisa tanadin doka dangane da takardar sammaci da kotu ta fitar a baya haryanzu yana tafiya.
