News
Gwamnati Za Ta Fara Yi Wa Yara Allurar Rigakafin Zazzabin Cizon Sauro
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta Kasa NPHCDA ta bayyana cewa gwamnati za ta fara yi wa yara allurar rigakafin zazzabin cizon sauro a jihohin Kebbi da Bayelsa daga ranar biyu ga Disamba.
Yin hakan na daga cikin matakan da gwamnati ta dauka domin gamawa da cutar dake yaduwa kamar wutar daji take kashe mutane a kasar nan.
Shugaban hukumar NPHCDA Muyi Aina ya sanar da haka wa manema labarai a Abuja.
Aina ya ce za a yi wa yara kanana ‘yan kasa da shekara biyar allurar rigakafin kyauta a wadannan jihohi.
Ya ce ma’aikatan lafiya za su rika bin mutane gida-gida, asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko dake wadannan jihohin domin yi wa yara rigakafin cutar.
Aina ya ce gwamnati na da burin yi wa yara miliyan 1.5 allurar rigakafin cutar a wadannan jihohi.
Ya ce baya ga allurar rigakafin gwamnati za ta hada da sauran matakan dakile yaduwar cutar da suka hada da raba wa mutane gidajen sauro da bada magungunan cutar kyauta.
Aina ya ce gwamnati za ta yi haka ne tare da hadin gwiwar UNICEF da WHO.
“Gwamnati na da burin ganin ta rage yaduwar cutar zuwa kashi 40% a Najeriya nan da 2030.
Shugaban hukumar ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara a wadannan jihohi da su tabbatar sun mika su an yi musu rigakafin.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
